Malaman Addinai A Najeriya Sun Gudanar Da Addu'o'i Na Musamman

Matasa A Najeriya

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke gabatowa a Najeriya, shugabannin addinai sun dukufa wajen gudanar da adduo'i na musamman domin ganin an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Dalili kenan da malaman addinin musulunci a jihar Neja suka hadu domin gudanar da adduo'i neman biyan bukata. Malam Muhammadu Sanusi Erana ya bayyana dalilin su na yin hakan, inda yace suna neman zaman lafiyar kasa da taimakon Allah a zabe mai zuwa.

Sun kuma gabatar da bukatar su a wajen shugabannin siyasa da su daina amfani da matasa wajen tada hargitsi domin biyan bukatar su kawai.

Bishop Tukura ma ya bayyana yadda suka gudanar da addu'oi tare da yin azumi na musamman domin samun zaman lafiya.

Domin jin karin bayani, saurari raghoton Mustapha Nasiru Batsari...

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Addinai A Najeriya Sun Gudanar Da Adduo'i Na Musamman 2'57"