Malama Lantana: Sana'ar Cikin Gida Na Kauda Takaici Ga Mata

Lokaci yayi da matasa zasu tashi tsaye domin zama masu dogora da kai, tare da kauracewar yawan "bani-bani" da akanyi wa mai gida, da kauda kai ga kananan bukatu kamar yadda Malama Lantana Abdullahi ke fadi.

Ta fara wannan sana’ar ne kimanin shekaru 30 da suka wuce, inda ta fara da kananan kaya wanda ta fara saro su tun daga gida, daga bisani Allah ya yassare har ta fara fita wasu kasashen domin saro kaya, ta kuma sayarwa mata a gidajensu.

Ta faro ne da sana’ar sayar da atamfofi da wasu kayayyakin mata, daga bisani da sana’ar ta habbaka ne ta fara sayar da kayan gida, kamar su gadaje, da sauran kayan aure na mata.

Batun nan na bashi kamar kowanne mai irin sana’a yana da nasa kalubalen, kuma bashin nan sai da shi ne aka kafa sana’a. Ko da an karbi kayanta aka kuma ki biyanta akan lokaci, bata damuwa domin sana'ar ta gaji hakan.

Daga karshe Malama Lantana ta bukaci mata da su jajirce wajen kama kananan sana'o'i, a cewarta "sai an fara da karamar sana'a ne sannan ake zuwa ga manyan sana'o'i."

Your browser doesn’t support HTML5

Malama Lantana: Sana'ar Cikin Gida Na Kauda Takaici Ga Mata 2'30"