Dan wasan tsakiya na Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea N'Golo Kante, dan kasar Faransa na shirin sabunta kwantirakinsa a kulob din.
Danwasan Kante ya bayyana jin dadinsa da wannan damar da Kungiyar ta Chelsea ta bashi na karin wa'adin zamansa inda zai dinga karban fam dubu 300 duk shekara a matsayin albashi maimakon 150 da yake amsa tun da yazo Kungiyar daga Leicester City a shekara 2016.
Kungiyar ta Chelsea ta ce takardan yarjeniyar a yanzu haka ya na hanun lawyar kulob din kafin a bayyana shi a hukunce.
Kante ya samu nasarar lashe gasar firimiya lig sau biyu a jere, daukar farko tare da tawagar Leicester City, sai kuma a shekarar da ta zagayo ya sake samun nasarar lashe kofin a Kungiyar Chelsea, bayan ya dawo kulob din akan kudi fam miliyan 30, na tsawon shekaru 3.
Yanzu dan wasan zai sanya hanune a Chelsea na tsawon shekaru biyar, zai bar kulob din yana da shekaru 32 kenan.
Kafin wannan lokaci Kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa ta nuna sha'awarta na ganin ta dauki dan wasan Kante mai shekaru 27 da haihuwa.
Facebook Forum