Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Sallar Cika-Ciki A Amurka, Ya Take Gudana?


Sallar cika ciki a Amurka na iya zama sallar da tafi kowace samar da nishadi, da kuma aiwatar da wasu abubuwa da mutun baiyi suba a duk ilahirin shekarar.

Bukin sallar cika ciki a Amurka ta samo asaline tun a shekrar 1621, kimanin shekaru 397, kenan da aka fara gudanar da wannan bukin, a duk ranar Alhamis ta uku a watan Nuwambar kowace shekara.

Amurkawa kan gudanar da bukin, wanda iyalai kan hadu a ci abinci tare, don yima Allah godiya, da nuna jin dadin su ga Allah da ya basu lafiya da ikon ganin zagayowar ranar.

Sallar na daya daga cikin manya-manyan bukukuwa da ake gudanarwa a kasar Amurka, dangi daga ko’ina suna halartar bukin don ganawa da ‘yan uwa, da saye-saye don bada kyauta ga marasa hali da ma ‘yan uwa da abokan arziki.

Lokacin bukin Amurkawa da ma wasu ‘yan kasashen waje sukanyi amfani da lokacin don yin saye-saye, kaya nayin sauki ga duk mai bukata. Duk gidajen abinci sukan rage kudin abincinsu a wannan rana, don saukakama jama’a.

A lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln a shekarar 1863 aka ayyana wannan bukin a matsayin hutun kasa baki daya, itace kuma ranar da ake mata kirari da ranar Talo-Talo, don shine naman da akafi ci sai kuma Alade.

A cewar kungiyar masu saida Talo-Talo ta kasa a shekara da ta gabata an saida Talo-Talo kimanin milliyan 44, a ranar bukin cika cikin, yau da misalin karfe 12:00pm har zuwa tsakiyar dare za ayi ta tande-tande da lashe-lashe a baki dayan kasar Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG