Wani Lauya Yace Fadar Shugaba Tana Yin Bi-Ta-Da-Kulli, Amma...

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Sarki

Mallam Garba Shehu yayi watsi da batun yin bi-ta-da-kulli musamman ma shugabannin majalisar dattawa, yana mai cewa atoni-janar yana da hurumin gurfanar da duk wanda ake tuhuma a gaban kotu.

Yayin da ake ci gaba da cacar-baka tsakanin fadar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da kuma shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki, yanzu haka masana harkar sharia’ da kuma siyasa na ganin akwai bukatar karatun ta natsu.

A jiya Litinin ne dai aka gurfanar da Bukola Saraki da mataimakinsa, Ike Ikweremadu, da wasu mutum biyu a gaban wata kotun dake Abuja, inda ake zarginsu da yin jabun dokokin majalisar dattawan.

Tun farko ma dai sai da Saraki ya yi zargin cewa wasu mutane sun kwace ikon tafiyar da kasar daga hannun Shugaba Buhari batun da ko hadiman shugaban kasan ke musanatawa.

To ko me masana harkar sharia ke cewa game da wannan sabon dambarwa? Barr.Sunday Joshua Wigra, wani masanin shari’a ne a Najeriya. Yace abun takaici ne ma da wasu batutuwa suka fito fili, a yayin zaman kotun da aka yi a jiya, wanda hakan ka iya nunin da wata sabuwa,wai in ji yan caca. A ganinsa, batun kada a bayar da belin mutanen ma da aka tayar, watakila yana nuni da wata kullalliya.

To sai dai kuma a martanin da shugaban Najeriyan ke maidawa ta bakin hadimansa shugaba Buhari ya musanta wannan zargi na ''bi-ta-da-kulli'' da ake zargin yanayi.

Mallam Garba Shehu, hadimin shugaban kasar ne ta fuskar harkokin yada labarai. Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Ministan shari'a, wanda kuma shi ne babban lauyan gwamnati, damar shigar da karar duk mutumin da ya aikata laifi domin a hukunta shi.

Saurari cikakken rahoton...

Your browser doesn’t support HTML5

Martani Kan Tsama-Tsakanin Saraki Da Fadar Shugaban Kasa - 5'25"