Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Bar Wasu Sun Kwace Ikon Mulkinsa-Saraki


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

A wata wasika da shugaban majalisar dattawan Nageriya ya aikawa shugaban kasa Muhammad Buhari, wadda aka rabawa manema labarai, ya zargi shugaban da yin sakaci da inkonsa inda, wai, har wasu sun kwace ikon suna yin abun da suka ga dama

Bukola Saraki ya yi la'akari ne da tuhumar da bangaren zartaswa ke yi masa tare da mataimakinsa inda yace wasu kalilan da basu san yadda ake gudanar da ayyukan majalisa ba ke bin son zuciyarsu domin cimma wani buri na daban.

Kalamun na Bukola Saraki ba zasu rasa nasaba da tarurrukan da 'yan majalisar dattawan suka yi ba, har suka yi barazanar janye goyon bayansu ga bangaren gwamnati. Emmanuel Bwacha dan jam'iyyar PDP ne a majalisar, kuma shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar.

Yace a matsayinsa na mataimakin shugaban marasa rinjaye sun ga canje canjen da ake son ayi basu cancanta ba. Sun ja kunnen majalisar zartaswa cewa su bari, kada su shiga harkar majalisa. Wato ana kokarin a tsige shugaban majalisar da mataimakinsa. Yace babu zato ba tsammani sai kawai suka ji za'a kai shugabannin biyu kotu. Yace wannan wani sabon yunkuri ne na cire su mutanen biyu lamarin da ya kwana biyu ana ta kokarin yi.

Jin cewa shugaban majalisar ya rubutawa shugaban kasa akan abun dake faruwa sai 'yan jam'iyyar APC mai mulki da na jam'iyyar Labor suka ce ra'ayinsu ya sha banban.

Aliyu Malam Wakili na APC yace sun fito ne su numa goyon bayansu ga shugaban kasa, su tabbatar masa cewa canjin da yake bukata zasu tabbatar ya wakana. Yace da lallashi da hadin kai da abokan hamayyarsu, wato PDP, zasu cimma nasara domin sun ba APC hadin kai tun farko.

Korafe korafen sun samo asali ne saboda karar da ministan Shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya shigar a kotu inda gwamnatin tarayya ke tuhumar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon magatakardar majalisar Salisu Maikasuwa da tsara wasu dokokin jabu a majalisar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG