Tun bayan sace yaran da wasu malamai abinda ya dauki hankalin al'ummar duniya, har yanzu jama'a sun kasa kunne tare da zura ido domin ji ko ganin abin da zai faru musamman duba da cewa an saba sace dalibai kuma a sako su bayan gwamnati ta tsoma hannun ta.
Haka ma goron gayyata da gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya mika na kiran gayya domin shiga daji ya zaburar da kungiyoyi da al'umomi daban-daban suna nuna goyon bayansu ga wannan lamarin.
Wannan karon kungiyar Miyetti Allah ce ta Najeriya ta jaddada goyon bayanta ga duk matakin da za'a dauka don ceto yaran.
Shugaban kungiyar na kasa Muhammadu Kiruwa wanda ya nuna rashin gamsuwa ga yadda ake kebe kabilar Fulani ga aikata ta'addanci wanda ya ce a kowace kabila ana iya samun dan ta'adda, ya ce Fulani sun shirya su shiga a yi da su.
Sai dai sabanin yadda jama'a suka fahimci kalaman gwamna Bagudu, ba gayya ce ta shiga daji ba a cewar sa.
Duk da kalaman da hukuma ke yi na cewa ana kan kokarin ganin an sako yaran, har yanzu wasu iyaye hannun na gaba muddin ba ‘ya'yansu suka gani ba kamar yadda wasunsu suka nuna.
A can yankin da ake tunanin ana tsare da yaran kuwa mun tuntubi wani mazaunin wurin wanda ya ce mutane yanzu sun fara dawowa daga gayyatar su.
Satar dalibai a Najeriya dai abu ne wanda mutane da yawa ke kallon sa a zaman wata makarkashiya ta jefa tsoro cikin zukatan jama'a da kuma kara gurgunta harkar ilimi musamman a yankin arewa wanda sai gwamnati ta yi da gaske don shawo kan matsalar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5