Wasu manyan arewacin Najeriya sun fito sun yi kira ga matasa, su guji tayar da hankali da yin jafa'i a lokacin zabe. Daga cikin wadanda suka yi wannan kira, wasu sun kara jaddadawa matasa cewa su lura da masu ingiza su, su gani ko su na hadawa har da 'ya'yan su.
Janar Mahammadu Buhari dan takarar shugaban kasar a karkashin laimar jam'iyar hamayya ta APC yayi karin hasken cewa, kalmomin yakin neman zaben da yake yin amfani da su na "a Kasa, a Tsare, a Raka, a Jira", ba kalmomi ba ne na kiran magoya bayan shi su yi rikici ko kawo tashin hankali.
Daga cikin masu yin wannan kira ga matasa akwai kungiyoyin rajin ci gaba da na matasan su kan su, da dattawa, da shugabannin addinai, da Masarautun gargajiya.
Babban sakon da ake kokarin isarwa matasa shi ne su guji tarzoma a lokacin zabe da ma bayan an kammala zaben.
An yi wannan kira ga matasa ne dai ana sauran kasa da makonni biyu a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, kuma a yayin da ra'ayoyi suka sha bamban tsakanin masu so a yi zabe, da wadanda ke so a dage shi.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ne ya aiko da wannan rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5