Janaral Mansur Dan Ali mai ritaya yace duk wani tsohon soja kamarsa ya san suna son kasa ta kasance a dunkule, tsintsiya madaurinki daya.
Amma wasu abubuwa na faruwa da ba daidai ba ne. Sun nuna babu kishin kasa. Si ya sa dole mutane su fito su nuna bacin ransu. Abubuwan dake faruwa a kasar bai kamata a ce suna faruwa ba. Rashin zaman lafiya na cikin abubuwan dake damun mutane yanzu.
Dangane da taron kasa da za'a yi yace taron nada mahimmanci domin ya kunshi tsoffin shugabannin kasa da gwamnoni. Nan ne zasu duba abubuwan dake faruwa a kasar musamman batun yiwuwar yin zabe a lokacin da doka ta tanada.
Bayanan jami'an tsaro da na hukumar zabe su ne zasu taimaki taron ya tsayar da shawara akan zaben. Amma shi Janaral Mansur yace inda yana cikin taron ba zai bada shawara a dage zaben ba saboda abun da jama'a suke so shi yakamata a yi.
Akan raba katin zabe Janaral Mansur yace an kara mako daya idan kuma ana so ana iya bin mutane gida gida a rabasu. Kada a labe da batun tashin bama bamai domin yanki guda ne ake samun tashinsu. Idan an sake dubawa shi ma lamarin tashin bama bamai yana da ma'ana. Ana neman ko wani abu zai taso a ce zaben ba zai yiwu ba.
Janaral Mansur Dan Ali yace masu son a dage zaben ba komi ba ne illa son rai ne. Don haka maganar dage zabe bata ma taso ba domin ba kasar gaba daya take yaki ba.
Akan masu cewa idan dan takararsu bai ci zabe kasar zata wargaje, Janaral Mansur yace basu san yaki ba ne. Masu maganar kananan yara ne. Yayin da irinsu Janaral Danjuma, wanda yanzu suke zagi, suka sadakar da rayukansu domin kare kasar, su ba'a ma haifesu ba. Irinsu jikoki su ke ga Janaral Danjuma. Amma yau su ne suke zaginsa saboda rashin kishin kasa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.