A safiyar yau Talata, koriya ta arewa ta gudanar da gwajin makami mai linzami wanda ya ketara ta sararin saman kasar Japan, wanda masu fashin baki suka kwatanta da irin wanda kasar ta fara barazanar gwadawa, da take cika bakin cewa zai iya kaiwa wani yanki na Amurka.
Lamarin da ya haifar da mayar da martanin ‘yan kasar ta Japan, da sauran shugabanni.
An yi imanin wannan shine gwajin makami mai linzami da zai iya cin dogon zango tsakanin kilomita 3000 zuwa 5000 na biyu da ya sami nasara, a cewar kwararren masanin makamai masu linzami Jeffery Lewis, babban daraktan shirin bada gudummuwa na gabashin Asiya, dake makarantar nazarin harkokin kasa da kasa a jihar California.
A watan Mayu ne Gwajin makamin mai lakabin Hwason 12, na farko ya sami nasara.
Shugaba Donald Trump yayi Allah wadai da gwajin makamin da kasar Koriya ta arewa ta yi, da cewa kasar ta nunawa makwabtanta da dukkan mambobin majalisar dinkin duniya irin raunin da take da shi da kuma matsayinta na kin amincewa da halayen da suka dace na kasa da kasa.