Majalisun Dokoki Tamkar 'Yan Amshinshata Ne

Nigeria National Assembly

Nigeria National Assembly

Ana zargin majalisun Najeriya musamman na jihohi cewa tamkar 'yan amshnshatan gwamnoninsu ne.
Ana zargin majalisun dokokin Najeriya musamman na jihohi tamkar 'yan amshinshatan gwamnoninsu ne. Sai abun da gwamninisu suka so suke yi.

Wasu masana sun ce babu abun da 'yan majalisu zasu iya yi domin ba komi ya jawo hakan ba sai rashin hali. Gwamnoni da majalisar zartaswa ke da kudi da jami'an tsaro da duk wani madafin iko.

Kodayake dokar kasa ta ba 'yan majalisa ikon kula da ayyukan zartsawa da ikon tsige gwamna ko shugaban kasa idan ya wuce makadi da rawa to amma yawancin 'yan majalisun ba zabe suka ci ba. Gwamnonin suka tsaya masu har aka zabesu. Wasu ma duk gwamnoni ne suka dauki nauyin biyan kudin zbensu. Don haka da wuya su hukunta gwamnoni ko su ja masu birki idan suna son su wuce gona da iri. Sau da yawa 'yan majalisun su kan zama 'yan amshinshatan gwamnoni iyayen gidansu wadanda suka kawo su siyasa suka sa su zama 'yan majalisu.

Wani masani Dr Sa'idu Abubakar ya bayyana cewa yawancin 'yan majalisu basu ci zabe ba. Gwamnoni suka dorasu don haka ya zama wajibi a kansu su yi yadda gwamnonin suke so domin kowa ya ci ladan kuturu to dole ya yi masa aski.

To sai dai wasu 'yan majalisu sun ce kowa ya ce su 'yan amshinshata ne su bai yi masu adalci ba kamar yadda kakakin majalisar Neja Alhaji Adamu Usman ke cewa. Ya ce idan akwai zaman lafiya a jiha domin kowa na aiwatar da aikinsa kamar yadda doka ta tanada sai a ce sun zama 'yan amshinshata. Ya ce idan sashen zartaswa ya bi doka su ma sun bi to menene zai jawo cecekuce?

Ladan Adamu Ayawa nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisun Dokokin Najeriya Tamkar 'Yan Amshinshata Ne - 4:21