Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shirya Gangamin Fadakar Da Matasa A Taraba


Matasa masu zanga zanga
Matasa masu zanga zanga

A Jihar Taraba an shirya gangamin fadakar da matasa domin su rugumi zaman lafiya.

A kokarinta na samarda zaman lafiya Jihar Taraba ta shirya gangamin fadakar da matasa wadanda su ne mutane ke anfani da su wurin haddasa rikici na kabilanci da addini.

A wurin taron fadakar da matasan gwamnan jihar ya nuna takaicinsa yadda wasu ke anfani da matasan suna tada fitina a jihar. Gwamnan wanda shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Injinya Ahmed Yusuf Gamaliel ya wakilceshi ya ce su je makarantar ta natsu. Ya ce matasa suna son su dauki abu da zafi-zafi kamar yadda su ma suka yi cikin kuruciya. Su duba, jihar na fuskantar matsaloli da yawa don haka kada su bari ana anfani dasu ana dada hura wutar rikici a jihar. Ya ce a kowane fanni a kasar, ba wai Taraba ba kawai ba, akwai damuwa. Haka kuma talauci ya yiwa kowa katutu.

A nashi jawabin shugaban matasan Najeriya reshen Taraba Mr. George ya gargadi gwamnati ta tashi ta samarma matasa abun yi. Rashin aikin yi shi ne ya sa wasu manayan mutane ke neman yin anfani da matasa su yi masu alkawarin basu kudade domin su aikata wasu abubuwan da basu da kyau. A nasu bangaren ya ce zasu yi kokari su tabbatar cewa matasa sun guje ma duk wani da zai rudesu da kudi su tada hankali. Zasu tabbatar matasa sun samu abun yi. Wanda kuma ya ke son tada hankali to ya yi anfani da nashi 'ya'yan.

A can baya kananan hukumomin Ibi da Wukari sun sha rikicin kabilanci da na addini. Shugaban karamar hukumar Wukari Isiaku Adamu ya gargadi matasa su dinga hakuri da juna musamman idan an saba masu. Idan ba'a hakura da juna ba to kullum za'a ta yin fada ana tada hankali. Idan aka yi fada aka kashe mutum to daukan ramako zai kara daukan rai ne. Idan ma gida aka kone kana aka ce za'a yi ramako to wani gidan kuma za'a kone. Don haka ya zama wajibi a yi hakuri da juna a dinga neman yin sulhu idan wani abu ya taso.

'Yan rajin kare hakin bil adama da neman adalci sun ce duk wani musulmi dake kashe mutane ko tada hankali ba musulmin kwarai ba ne. Haka ma kristan dake tada hankali yana kone-kone idan an bincika ko mijami'ar ma baya zuwa. Don haka a kiyaye a lura kada a fada tarkon irin wadannan miyagun mutane. Kowa ya yi addinin da yake so ba tare da tsangwama ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG