Majalisun Amurka Sun Dage Tattaunawa A Kan Batun Kudaden Gudanar Da Gwamnati

Taron Hadin Gwiwar Majalisun Amurka

Yayin da ake yita kai ruwa rana tsakanin majalisun Amurka da shugaba Donald Trump a kan batun kudaden gina katangar kan iyaka, majalisar dattawan Amurka ta dage zamanta a jiya Asabar da rana zuwa ranar Alhamis.

Rufe wani bangaren ayyukan gwamnati da ya fara aiki a da misalin karfe 12 na tsakiyar daren Asabar, shine ya hana majalisun kasar daukar matakin bada kudaden da zai sa gwamnatin ta ci gaba da aiki.

Rufe gwamnatin ya shafi kimanin kashi 25 cikin dari na ayyukan gwamnati, lamarin da ya addabi ma’aikatan gwamnati dubu dari takwas, kana rabin wannan adadi kuma zasu yi aiki ba tare da samun biya ba.

Jim kadan kafin shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa Mitch McConnell ya sanar da dage zaman majalisar zuwa ranar 27 ga wannan watan Disemba, manema labarai sun ce mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya je majalisa domin ya tattauna da shugaban marasa rinjayi a majalisar dattawa Chuck Schummer.

Da safiyar Jiya Asabar shugaba Trump ya tattauna a kan batun tsaron iyaka da ‘yan majalisa na bangaren jami’iyarsa ta Republican da wasu manyan jami’an fadar White House kana sun tattauna batun kudurin kashe kudaden gwamnati ciki har da batun dala biliyan biyar na gina katangar kan iyakar Amurka da Mexico.