Majalisar Wakilan Amurka mai rinjayen 'yan Republican, ta kada kuri'ar amincewa ta wuccin gadi, kan wani kasafin kudi wanda ya tanadi dala biliyan 5 na gina katangar da Shugaba Donald Trump ke son yi.
Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da kuri'u 217 akasin 185, da daren jiya Alhamis, da zummar kauce ma yiwuwar tsai da ayyukan gwamnati da karfe 12 na daren yau Jumma'a.
Yanzu za’a tura kudurin kasafin kudin zuwa Majalisar Dattawa, inda ga dukkan alamu ba zai samu amincewa ba.
Trump ya bukaci kudin ne don gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, ya na mai gaya ma 'yan Republican da ke Majalisar Wakilai tun jiya Alhamis cewa ba zai sa hannu kan duk wani kasafin kudin da Majalisa ta gabatar wanda bai tanadi kudin gina katangar ba.
Facebook Forum