Sojojin wanzar da zaman lafiya guda hudu ne 'yan bindiga suka kashe a kudu maso gabashin Afrika ta tsakiya.
WASHINGTON D C —
Babban sakataren Majalissar Dinkin Duniya Antonio Guterres, yayi Allah wadai da kisan da akayi wa sojojin kiyaye zaman lafiya guda hudu a Junhuriyar Afirka Ta Tsakiya, biyo bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin su, wanda ake zargin ‘yan tsagerun Anti-Balaka ne suka kai shi.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na MINUSCA ne ya bada tabbacin mutuwar Sojan Wanzar da Zaman lafiya guda daya dan asalin kasar Cambodia. Daga baya ofishin ya kara tabattarda mutuwar karin sojoji ukku daga cikin hudun da suka salwanta. Daga baya aka same su sun mutu.
An dai kai harin ne a kusada kauyen Yogofongo, Mai nisan fiye da tazarar Kilomita 470 da ta raba shi da Bangui, babban birnin Junhuriyar Afirka Ta Tsakiyar.