Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Cuta Mai Saurin Kisa Ta Bulla a Liberia


Kwayar halittar dake hadda sabuwar cutar dake da alajabi
Kwayar halittar dake hadda sabuwar cutar dake da alajabi

A kasar Liberia wata cuta mai al'ajabi ta bulla har ta kama mutane fiye da talatin inda goma sha uku cikinsu suka rigamu gidan gaskiya cikin makonni biyu kacal

Wasu kwararrun jami’an kiyon lafiya na Amurka sunce wata cuta mai ban mamaki da ta bayyana a kasar Liberia, har ta kashe mutane 13, cuta ce da ake samu daga wani sinadari dake haifarda kwayar cuta mai kama da sankarau kuma mai kisa a cikin kwakwalar mutane.

Mutane akalla 31 suka kamu da wannan cutar a cikin makkoni biyu da suka gabata, kuma daga cikinsu ne mutane 13 suka rasa rayukkansu.

Rahottani sunce an aika samfurin wasu sassan jikin 4 daga cikin mutanen da suka rasu zuwa Cibiyar yaki da Cuuttutukka ta Amurka (CDC) ta Amurka don gudanarda bincike.

Jami’ai a can Liberia sunce aksarin mutane 31 da suka kamu da wannan cutar duk mutane ne da suka halarci jana’izar wani shugaban addini da ya rasu ne a can Liberia a ran 22 ga watan Aprilun da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG