Fadan dai ya fara ne tun daga sanyin safiya, lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari sansanin sojin Somali da ke gundumar Goofgaduud, mai tazarar kilomita 35 daga Baidoa, wadda kuma ke da tazarar kilomita 250 daga babban birnin Mogadishu.
Kamar yadda wani da ya shaida faruwar lamarin ya fadawa Muryar Amurka, yace “kusan zaratan mayakan ‘yan ta’adda 100 dauke da makamai suka afkawa sansanin. Fadan dai kwashi kusan awa ‘daya ana yi. Inda suka tilastawa sojojin gwamnati ficewa daga sansanin, amma suka koma ba tare da bata lokaci ba.”
Shima wani da ya shaida lamarin ya ce yaga gawarwakin ‘yan ta’adda 4 da kuma na sojojin gwamnati 3 suna kwance kan titi.
Facebook Forum