Shugaban mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan ya yi taron ne a shirye-shiryen da ya keyi na mika shugabanci ga Janar Buhari gobe Juma'a idan Allah Ya yadda.
A wurin taron ministocin da shi shugaban mai barin gado sunyi ta goga kansu na nuna irin nasarorin da suka samu da dimbin aikin da suka ce sun yiwa Najeriya. A nasu ganin kwaliya ta biya kudin sabulu.
Bayan taron wakilin Muryar Amurka yayi fira da karamin ministan kudi Alhaji Bashir Yuguda domin jin abubuwan da zai fada akan tabarbarewar tattalin arzikin kasar da dimbin bashi da rashin kudi da talaucin da ake cewa sun addabi Najeriya daidai lokacin da suke shirin mika mulki.
Akan batun asusun Najeriya da zargin cewa kasar ta talauce ya ce sun yi wannan bayani a rubuce ba sai ya yi magana ba. Dangane da bashi yace akwai na jihohi da na gwamnatin tarayya. Akwai basussuka da aka ci na cikin gida da na kasashen waje. Yace akwai bashin da aka dauka da za'a yi shekaru arba'in ana biya. Irinsu ne aka tattara aka hada cikin rahoton gwamnati aka ce ana bin Najeriya dala biliyan sittin. Ministan ya ki ya amsa wasu tambayoyin.
Amma dan takarar mukamin shugaban kasa na jam'iyyar ADC Dr. Mani Ibrahikm ya yi tur da Allah wadai da duk jami'an gwamnati dake cewa komi na nan lafiya kuma zasu mika mulkin kasar ba tare da wasu matsaloli ba. Yace maganar ministocin maganar banza ce kuma ta rashin hankali. Yace ko tantama babu gwamnatin Jonathan ta gurguntar da kasar. Kudaden da ake ajiyewa domin koda ta kwana duk babu su.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5