Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta jingine cigaba da naziri da tattaunawa akan batun sabon mafi karancin albashi domin baiwa Shugaban Kasa Bola Tinubu damar fadada tuntuba da masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, shugaban kasar yayi nazarin rahoton da kwamitin nan me bangarori 3 ya gabatar masa akan mafi karancin albashi kuma zai cigaba da tuntuba akansa kafin gabatar da matsayar karshe kan batun gaban Majalisar Dokoki.
An jima ana takaddama akan mafi karancin albashin ga ma'aikatan gwamnatin Najeriya.
Wa'adin dokar mafi karancin albashi ta 2019, data tsayar da mafi karancin albashi akan Naira dubu 30, ya kare a watan Afrilun daya gabata. Kamata yayi a rika sabunta dokar duk bayan shekaru 5 domin dacewa da bukatun tattalin arzikin ma'aikata na wannan lokaci.
A watan Janairun daya gabata Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti me bangarori 3 domin tattaunawa akan sabon mafi karancin albashin ma'aikata.
Kwamitin ya kunshi wakilan hadaddiyar kungiyar kwadago dana gwamnatocin tarayya dana jihohi da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.