Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) tace kananan hukumomin kasar ba zasu iya biyan mafi karancin albashin da hadaddiyar kungiyar kwadago ta gabatar ba.
Shugaban ALGON na kasa, Aminu Mu’azu Maifata, ne ya shaidawa sashen kasuwanci na shirin tashar talabijin ta channels na sassafe mai suna “Business Morning” a yau alhamis.
Ya kara da cewar, da irin kaso dake zuwa daga asusun tarayya, babu karamar hukumar da zata iya biyan naira dubu 62 a matsayin mafi karancin albashin da gwamnatin tarayya ta gabatar ballantana naira dubu 250 da hadaddiyar kungiyar kwadago ke bukata.
Mu’azu-Maifata ya cigaba da cewar har yanzu wasu kananan hukumomin basu fara biyan ma’aikatansu naira dubu 30 din da aka amince a matsayin mafi karancin albashin a 2019 ba.
ya cigaba da cewar a galibin kananan hukumomin, har yanzu ana biyan ma’aikata naira du 18 a matsayin mafi karancin albashi.
Maifata yace kamata yayi a biya mafi karancin da za’a iya ba wai wanda ba zai dore ba.
Dandalin Mu Tattauna