Bai daya Majalisar wakilan kasar Britaniya tayi na’am da shirye shiryen fadada filin sauka jiragen sama na Heathrow, filin saukar jiragen sama mafi girma a turai bayan an yi shekara da shekaru an yin muhawara akan irin tasirin da daukan wannan mataki zai yi.
Jiya Litinin Majalisar da ake cewa House of Commons ta jefa kuri’a dari hudu da goma sha biyar na amincewa gina hanyar saukar jiragen sama ta uku a Heathrow.
Gwamnatin Prime Minista Theresa May ta masu ra’ayin rikau da kungiyoyin yan kasuwa sun goyi bayan daukan wannan mataki sosai..
Gwamnati ta lashi takobin cewa zata fadada filin saukar jiragen sama ba tare da an taba aljihun yan kasar ba, ma’ana ba tare da an taba harajin da mutane suke biya ba, kuma matakin zai samar da aiyukan yi dubu dari.