Majalisar Wakilan Amurka Na Shirin Gabatar Da Kudurin Tsige Shugaba Trump

.

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ce yau Litinin 'yan majalisar wakilai zasu gabatar da kudurin neman majalisar ministocin Trump ta yi amfani da dokar nan ta 25th Amendment, da ta bada dama a sauke shugaba daga mukaminsa. 

A wata wasika da ta turawa abokan aikinta 'yan Democrat, Pelosi ta ce idan mataimakin shugaban kasa Mike Pence bai dauki wani mataki cikin sa’o’i 24, majalisar wakilan za ta ci gaba da shirin tsige shi.

“Don kare dimokradiyya da kundin tsarin mulkinmu, za mu dauki matakin gaggawa, saboda shugaban na zaman barazana ga dukkan biyun. Yayin da kwanaki ke wucewa, tashin hankalin farmakin da aka kai kan dimokradiyyarmu da wannan shugaban ya haddasa, ya karu don haka muke bukatar daukar mataki ba tare da bata lokaci ba, a cewar wasikar.”

Kokarin sauke shugaba Trump daga mukaminsa a kwanakin karshen mulkinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun kiraye-kirayen a dora alhakin harin da aka kai kan dimokradiyyar kasar ranar Larabar da ta gabata akansa, lamarin da ya yi sanadiyyar kisan mutane 5 a ginin majalisar dokokin Amurka a lokacin da masu tarzoma da ke goyon bayan Trump din suka afka ginin.