Majalisar Wakilan Najeriya ta zartar da kudirin matsakaicin kasafin kudin 2025 zuwa 2027 zuwa doka.
Yayin zartar da matsakaicin kasafin kudin, Majalisar ta bukaci kwamitocinta a kan kudi da hakar danyen mai da cinikin albarkatun man fetur su binciki rahoton da hukumar rabon arzikin kasa dake zargin kamfanin man Najeriya (NNPCL) da rike Naira tiriliyan 8.48 a matsayin kudaden tallafin man fetur din da aka karba.
Haka kuma, binciken zai duba matsalar da rahoton hukumar dake kokarin tabbatar da gaskiya da adalci a harkar hakar ma’adinan Najeriya (NEITI) ta bayyana ta cewa NNPCL ya gaza biyan dala biliyan 2 (kwatankwacin Naira tiriliyan 3.6) na kudaden harajin da ya karba ga asusun gwamnatin tarayya.
Har ila yau an umarci kwamitocin su fayyace jumlar kudaden shigar (da suka karba) daga cinikin man fetur din da NNPCL ya yi tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.