Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Rashin Abinci A Najeriya


Nigeria Climate Food Security
Nigeria Climate Food Security

Wani bincike ya bayyana cewa rashin tsaro da hauhawar farashin kayan masarufi ya jefa 'yan Najeriya sama da miliyan 31 cikin matsanancin rashin abinci.

Sama da ‘yan Najeriya miliyan 31.8 ne suke fama da tsananin rashin abinci a sanadiyar kalubalen rashin tsaro da sakamakon cire tallafin man fetur, bisa bayanan gwamnatin kasar a jiya Talata wanda ta dogara da alkaluman da kungiyoyin kasashen duniya da dama da take hadin gwiwa da su a kasar.

Wata sanarwar da ma’aikatar kasafin kudi da tattali arziki ta fitar tace Kungiyoyin ne suka bayyana tsananin matsalar da ya haifar da rashin abincin tsakanin mata da yara a wurin wani taron da sukayi da gwamnati tsakanin ranar Litinin da Talata.

Binciken da hukumar MDD dake kula da wadatar abinci a duniya ta ce an samu karin mutane miliyan 18.6 da zasu fama da matsanancin rashin abinci daga watan Oktoba zuwa Dizamban 2023.

Ma’aikatar ta ce “tashin gwauron zabi da farashn kayan abinci suka yi, ya faru ne a dalilin cire tallafin man fetur baya ga kalubalolin tsaron da ake fama da su a kasar ne suka jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin wannan mayuwaci halin.”

Hare haren barayin daji dauke da bindigogi da adduna ya tilastawa manoma da dama kauracewa gonakin su, lamarin da ya dada haifar da tsadar kayan abinci da kayan masarufi yayin da Najeriya take fama da tabarbarewar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru.

Kungiyoyin kasashen duniya irin su UN Food and Agricultural Organization, the Global Alliance for Improved Nutrition da German Development Agency GIZ ne suka gudanar da binciken.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG