Daga garin Oshogbo babban Birnin jihar Osun, wata kotun tarayya ta ba majalisar dokokin Nigeria umurnin tsige shugaba Muhammad Buhari bisa wasu hujjoji guda uku.
Kotun tace shugaba Buhari ya gaza wajen hana kashe-kashen da ake yi a kasa. Na biyu wai shugaban ya kashe wasu kudade ba tare da izinin majalisa ba. Sannan hujja ta uku wai shugaban bashi da takardar shaida ta gama karatu.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Nigeria Senata Ahmed Ibrahim Lawal ya tambaya a ina kotu ta samo hujjojinta. Ya yi Allah wadai da kotun saboda, alkalin da ma’aikatan da wanda ya kai karar basu san abun da su keyi ba. Kotu bata da hurumi ta ce majalisa ta cire shugaban kasa. Majalisa ce take da hurumin yin hakan. Ya ja kunnen alakalai tare da kiran alkalin alkalan Nigeria da ya yi maza ya cire irin wadannan alkalan saboda basu san aikinsu.
Haka a majalisar wakilai Ahmad Babba Kaita y ace hukuncin abun dariya ne, kuma abun takaici ne a ce irin wannan hkumcin ya fito daga kotu, kotu kuma ta tarayya. Batun. Y ace babu gaskiya akan cewa Shugaba Buhari ya kashe kudi ba bisa ka’ida ba, watakila jahilci ne ya sa haka.
Sanata Suleiman Nazir yace, shugaba Buhari ba yi laifin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba. Sai dai saboda siyasa ka ce na ce za’a ci gaba da yi amma maganar mafarki irin ta kotun ne ba zasu yadda da it aba. Y ace dole ne su kare mutuncin Shugaba Buhari, da jam’iyyarsu kuma muddin suna cikin majalisa babu wanda ya isa ya kawo irin wannan maganar.
A saurari rahoton Medina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5