Majalisar ta yi gargadin cewa akwai hatsarin sake bullar cutar a wuraren da aka kawar da ita idan ba a gaggauta ja mata burki a wuraren da take yanzu ba
WASHINGTON, DC —
Majalisar koli ta yaki da Polio a duniya, ta yi gargadin cewa idan ba a yi hattara aka ja burki ma yaduwar cutar Polio gaba daya a duniya ba, akwai hatsarin yaduwarta sosai, duk da fatan da ake yi na kawar da sauran jinsuna biyu na cutar da ake gani.
A karshen wani babban taron da ta yi a New York, Majalisar kolin, wadda ta kunshi manyan cibiyoyin yaki da cutar Polio kamar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da asusun UNICEF da Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka, da Kungiyar Rotary, ta ce ana dab da kawar da jinsi na uku na kwayar cutar dake janyo shan inna, domin yanzu watanni 10 ke nan ba a samu irin wannan kwayar cutar ba.
Majalisar, wadda ta yi wannan zaman tare da wakilan kasashen da suka fi fama da wannan cuta, ta ce ta samu kwarin guiwar cewa an samu raguwar kashi 45 cikin 100 na bullar cutar Polio a Najeriya da Pakistan, idan an kwatanta da daidai wannan lokaci a shekarar da ta shige.
Amma majalisar ta ce a yanzu, samun nasarar shirin kawar da Polio ko shan inna daga duniya ya dogara ne kacokam a kan kawar da kwayar cutar a wasu yankuna kalilan na Najeriya da Pakistan inda har yanzu akwai ta.
Majalisar tana sake nazarin dabarun da ake amfani da su wajen yaki da cutar ta Polio a fadin duniya, kuma nan da wani dan karamin lokaci zata fito da sabbin dabarun takalar wannan cuta.