Wakiliyar asusun na UNICEF wadda ta fadi wannan a Sokoto lokacin wani taron shirya yaki da cutar Polio, ta ce a yanzu Najeriya ta shiga idanun duniya, kuma tana dab da kaiwa ga inda zata iya kawar da cutar nan.
Amma ta ce da yake da ma an ce in aski ya zo ga ban goshi ya fi zafi, yana da matukar muhimmanci ga dukkan masu ruwa da tsaki a wannan yunkuri su kara hada hannu da yunkurin kawar da wannan cuta.
Ta ce yana da matukar muhimmanci ga dukkan sassan su dafa domin a cimma nasarar kawar da wannan cuta.
Kwamishinan ayyukan kiwon lafiya na Jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya yaba da ayyukan da asusun na UNICEf yake yi.