A hirar shi da Muryar Amurka, Kansila mai wakiltar Mangu Ward 1, Kabiru Iliyasu ya bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda kasa aiwatar da wasu bukatu da majalisar ke ganin na ci gaba ne.
Da yake maida martini, shugaban karamar hukumar Mangu, Daput Minister Daniel yace rashin kudade a karamar hukumar ne ke kawo tarnaki ga aiwatar da bukatun ‘yan majalisar.
Shiko mataimakin shugaban karamar hukumar na Mangu, Alhaji Garba Hassan yace kansilolin basu bi doka wajen furta kalaman tsige shi ba, wanda yace ya gani ne a kafafen sada zumunta na zamani.
Daga karamar hukumar Jos ta Arewa ma, wasu ‘yan majalisar sun aike wa shugaban karamar hukumar, Shehu Bala Usman da takardar gargadi na tsigewa.
Mataimakin shugaban majalisar Jos ta Arewa, Auwalu Baba Ladan Garba yace suna zargin shugaban karamar hukumar ne da almubazaranci.
Shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman yace bai sami takarda daga ‘yan majalisar ba.
Lokaci ne kadai zai bayyana yadda za’a warware wannan dambarwa da bai zame wani sabon abu ba a lokaci na damokradiyya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5