Gwamnonin Najeriya Sun Kafa Kwamiti Ya Duba Yiwuwar Biyan Mafi Karancin Albashin Naira 60, 000

Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa gwamnonin sun kafa kwamiti da zai yi duba kan mafi ƙarancin albashi da jihohi zasu iya biya, kuma ya ce a shirye yake da yayi na’am da rahoton kwamitin.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce ta kafa kwamitin da zai yi duba kan mafi karancin albashi da jihohi zasu iya.

Gwamnan jihar Nasarawa ne ya bayanna wa Muryar Amurka haka yayin wata hira ta musamman da wakiliyar Sashen Hausa, Rukayya Basha, inda ya ce a shirye yake ya yi na’am da rahoton kwamitin.

A baya-baya nan ne Kungiyar ta ce biyan naira 60, 000 a matsayin mafi karancin albashi ba abu ne mai yiwuwa ba, sai dai wasu gwamnonin sun amince za su iya biya.

Daya daga cikinsu kuma gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya ce idan gwamnoni zasu tattara kuda den dake shigo musu, kuma zasu rage wadaƙa, to zasu iya biyan mafi ƙarancin albashin.

Sai kuma takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, wanda ya bayyana cewa jiharsa a shirye take ta fara biyan Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A watan Yunin da ya gabata ne Mukaddashiyar Daraktan yada labaran Kngiyar Gwamnonin Najeriya, Halima Ahmed, ta bayyana cewa biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 60,000 ga gwamnonin jihohi abu ne me wuya, saboda basu da isasshen kudin da biyan hakan zai ɗore.

Halima, ta ce sai dai gwamnoni suyi amfani da duk kudaden dake shigo musu daga Gwamnatin Tarayya wajen biyan albashin, wanda hakan ba zai basu damar yin sauran ayyuka ba.

Zauren Majalisar Gwamnonin, ta yi kira da kungiyar kwadago da ta takwarorinsu da suyi la’akari da kudin shigar dake shigowa jihohinsu, kuma su duba adadin mafi ƙarancin albashi da su gwamnonin zasu iya biya, wanda kuma zai ɗore, domin idan ba haka ba, wasu jihohin zasu kasance wajen rancen kudi domin biyan albashin.

Rilwan Ladan, ɗaya daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kullum, ya ce “ gwamnonin jihohi na da karfi da kuma kudin da zasu iya biyan Naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan kuma duk wani gwamna yace ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashin ba, to ya ajiye kujerar idan da gaske yake”.

A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Isa Abdullahi Kashere malami kuma masanin tattalin arziki dake Jami’ar Tarayya ta Kashere a jihar Gombe, ya ce “kudin shigar jihohi ya karu da kaso sama da 40, biyo bayan cire tallafin man fetur, wanda kuma hakan ya nuna cewa gwamnonin jihohi za su iya biyan adadin mafi ƙarancin albashin”.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Gwamnonin Najeriya Ta Bayyana Matsayinta Akan Biyan Mafi Karancin Albashi.mp3