Hadaddiyar kungiyar kwadago tace wa’adin mako guda data baiwa gwamnatin tarayya a talatar data gabata 4 ga watan Yunin da muke ciki, zai cika da tsakad daren gobe talata 11 ga watan na Yuni.
Kungiyar tace idan har gwamnatin tarayya da majalisar kasa suka gaza cika muradan ‘yan kwadagon zuwa gobe Talata, kungiyoyin kwadagon NLC da TUC zasu gana su yanke shawara akan cigaba da yajin aikin gama-garin da suka jingine a makon daya gabata.
Mataimakin Babban Sakataren Kungiyar Kwadago ta NLC, Chris Onyeka, ne ya bayyana wa tashar talabijin ta Channels hakan a cikin shirinta na sassafe mai suna “Borning bBrief” a yau litinin.
Jami’in kungiyar ta nlc ya kara da cewar, “gwamnatin tarayya da majalisar sun saurari bukatar, ba bukatar kashin kanmu bace. mun riga mun tura musu bukatunmu domin suyi nazari su kuma aika kudiri daga fadar shugaban kasa zuwa ga majalisar kasa, inda ita kuma majalisar zata nazarci bukatun namu da kuma abinda doka ta tanada, sannan su bullo da sabon mafi karancin albashi na kasa daya dace da bukatunmu.
“Idan har hakan taci tura, mun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin mako guda tayi nazari akan batun kuma a gobe Talata wa’adin zai cika. idan har bayan cikar wa’adin bamu ga wani takamaiman motsi daga gwamnatin ba, kungiyoyin dake cikin hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa zasu gana tare da yanke matakin da zasu dauka na gaba”.
Da ka tambaye shi matakin da kungiyar kwadagon zata dauka idan har gwamnati ta nace akan naira dubu 62, sai yace, “abinda muka fada a bayyane yake: mun jingine yajin aikin gama-garin da muka fara. Kamar misali ne ka dakatar da wani abu.
"Don haka, idan ka dakatar da wani abu kuma shugabannin dake jagorancin kungiyoyin kwadagon suka yanke shawarar rushe dakatarwar, hakan na nufin zamu koma kan abinda ya kasance a baya.”
Dandalin Mu Tattauna