Majalisar Dokokin Nijer Ta Sake Karatun Kasafin Kudin Shekarar 2021

Shugaban Niger Bazoum Mohamed

Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta sake yi wa tsarin kasafin kudaden 2021 karatu na 2 bayan da gwamnatin kasar ta bukaci a shigar da wasu kudaden tallafi da aka samar sakamakon yarjejeniyoyin da  aka cimma  a watan oktoban shekarar.

Sama da million 64,000 na CFA ne suka shiga aljihun gwamnatin Nijer ta hanyar yarjeniyoyin da ta cimma da bankin duniya da asusun lamani na IMF, da wacce aka saka wa hannu da kungiyar AFD, mafari kenan aka bukaci majalisar dokokin kasa ta yi wa tsarin kasafin 2021 sabon karatu domin shigar da wadann,an kudade ta yadda za a yi amfani da su wajen aiwatar da wasu aiyuka. Matakin da zai sa kasafin shekarar mai shirin karewa ya doshi billion 3,000 na CFA kamar yadda ministan kudin kasa Ahmed Djdoud ya bayyana.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta yi amfani da wadannan kudin billion sama da 64 a fannin tsaro da shirin tanadin cimakar da za a rarrabawa mabukata yayin da za a sayar da wani bangare akan farashi mai rahusa, sai wasu aiyukan gine-gine da tsarin kawata birane.

Majalisar ta amincewa kudurorin gwamnatin ta hanyar kuri’a inda daukacin ‘yan majalisar da suka hallara suka yi na’am da kuri’u 129 saboda abinda suka kira gamsuwa da kudurorinta, inji Honorable Issaka Assoumana, shugaban kwamitin kula da sha’anin kudi a majalisar dokokin kasa.

Wannan shi ne karo na biyu da majalisar dokokin Nijer ke yi wa kasafin kudin kasar karatu na biyu a bana sakamakon bukatun da suka taso. Sai dai zaman na wannan karon ya gudana ne a wani lokaci da ‘yan adawa ke kauracewa zaman nazarin kasafin shekarar 2022, saboda a cewarsu rashin yin bitar kasafin shekarar da muke ciki kafin fara nazarin kasafin shekarar da ke tafe take kundin tsrin mulki ne.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Nijer Ta Sake Karatun Kasafin Kudin Shekarar 2021