A jihar Neja, majalisar dokoki ta gayyaci kwamishanan 'yan sandan jihar ya bayyana gabanta ya bayyana mata matakan da yake dauka domin kawo karshen sace sace da kashe kashen mutane da ake yi a jihar musamman a yankuna biyu.
A cewar majalisar sace mutane domin neman kudin fansa na kara ta'azzara a jihar, musamman a yankunan Sarkin Pawa da Pandogari dake kan iyaka da jihar Kaduna. Lamarin na matukar tayar da hankalin majalisar.
Onarebul Sha'aibu Liman Iya shugaban kwamitin labarai na majalisar ya yiwa Muryar Amurka karin haske. Ya ce majalisa ta ga ya kyautu a gayyato kwamishanan 'yan sandan akan yawan sace sace da kashe kashen mutane a jihar. Lamarin tsaro ne da ya shafi kowa a jihar.
Kakakin 'yan sandan ASP Abubakar Dan Inna ya ce duk da cewa takardar gayyatar kwamishanan bata isa wurinsu ba amma suna da abun shaidawa majalisar akan sha'anin tsaron jihar.
A makon jiya rundunar 'yan sandan ta nunawa manema labarai wasu mutane 13 da ta zarga da kwarewa wajen yin garkuwa da mutane tare da yi masu kisan gilla.Cikin mutane akwai wani mai suna Lawal Kwali da aka ce shi ne shugaban muggan mutanen.
Lawal Kwalin ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya yi laifin kashe mutane. Ya amince da kashe mutane 30.
Ranar Litinin mai zuwa ne kwamishanan zai bayyana gaban majalisar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5