Wannan kuwa ya biyo bayan wasikar da ake zargin gwamnatin jihar ta aikewa rundunan yan sandan jihar na neman sakin wadanda ake tuhumar.
Shi dai wannan korafi, ya biyo bayan zargin cewa rundunan yan sandan jihar Taraban ta soma bin umarnin da gwamnatin jihar ta bata na sakin wasu da ake tuhuma da hannu a hare haren da aka kaiwa Fulani a tsaunin Mambilla da ya jawo asarar rayuka da dama.
Bayanai dai sun tabbar da cewa, kwamishinan shari’a kuma atoni janar na jihar Taraban, Mr Yusufu Akirikwen, shi ya aikewa kwamishinan yan sandan jihar wata wasikar da a shekarar data gabata yana neman a saki wadanda aka kama kan batun da yanzu haka allura ke neman tono garma.
A wajen wani taron manema labarai a Jalingo fadar jihar, hadakar kungiyar cigaban Taraba, ta Taraba Concern Citizen Forum, ta bukaci sufeta janar na yan sandan Najeriya da ya hanzarta bincikan wannan lamarin, don hukunta mai laifi.
Barr. M.B. Mustapha dake cikin shugabanin wannan kungiyar yace, sakin wadanda ake tuhumar na nuni da zargin da ake yi na cewa rundunan yan sandan jihar da bazar wasu suke taka rawa.
Facebook Forum