A wani taron manema labarai da kungiyar Afenifere ta kira a garin Akure baban birnin jihar Ondo ne ta kira ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali da ya sauka daga mukaminsa tare da kiran shugaba Buhari ya yiwa tsarin shugabannin tsaro garambawul ta yadda kowane bangaren Najeriya zai samu wakilci.
A cewar kakakin kungiyar Yinka Odumakin akwai gyara dangane da yadda harkokin tsaro ke tafiya a Najeriya musamman ganin yadda ake fadace fadace a jihohi daban daban. Sun ambaci fada tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihohin Binuwai da Nasarawa da Taraba da kuma Adamawa wanda inji kungiyar yaki ci yaki cinyewa.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu game da kiran da Afenifere ta yi. Alhaji Shettima Alfa Usman tsohon jami'in sojan tsaron Najeriya ya ce a saninsa shugaban koli na tsaro Bayerabe ne da sun ce shi ma ya sauka. Yakamata su yaba ma Mansur Dan Ali bisa ayyukan tsaro da ya yi a arewa maso gabas.
Sai dai a cewar shugaban kungiyar ta Afenifere Ayo Adebanjo akwai bukatar aiwatar da tsarin nan na yiwa Najeriya kanta garambawul.
Wasu 'yan Najeriya kuma na ganin matsayin kungiyar na kan turba. Inji wani kungiyar ta fadi ra'ayinta ne kawai idan kuma tana da hujja ta bayyana a gani. Wani kuma cewa ya yi 'yan arewa ne ya kamata su yi korafi akan tsaro saboda wai har yanzu abun da ya shafi harakar tsaro babu ci gaba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum