Majalisar Dokokin Najeriya na nazari a kan kudirin neman kara harajin cinkayya (VAT) daga kaso 7.5 cikin 100 zuwa kaso 10.
VAT shine harajin da ake caza a kan kaya ko aiki a dukkanin matakan da aka kara darajarsa.
A kudirin da ya fito daga bangaren zartarwa, majalisar na neman a kara harajin zuwa kaso 10 cikin 100 a shekarar 2025.
Haka kuma majalisar na shirin kara harajin na VAT zuwa kaso 12.5 cikin 100 tsakanin shekarar 2026 zuwa 2029.
Za a caji VAT a kan kayayyakin da suka cancanci harajin kamar haka (a) shekarar 2025 kaso 10% (b) shekarun 2026, 2027, 2028, 2029-kaso 12.5% (c) shekarar 2030 da bayanta kaso15%
A ranar 8 ga watan Mayun daya gabata, Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa a kan manufofin kudi da sauye-sauyen haraji, ya bayyana cewar akwai bukatar kara harajin na VAT.
A watan Satumba da ya gabata, Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun ya musanta rade-radin da ake yi na cewar an kara harajin cinikayya(vat) daga kaso 7.5 zuwa kaso 10 cikin 100.
A cewar Wale Edun, “har hanyu harajin cinikayya (VAT) na nan akan kaso 7.5 cikin 100 kuma shine abinda gwamnati ke caza akan cinikayyar wani rukunin kayayyaki da ayyuka da harajin ke aiki akansu. Don haka, babu ko guda daga cikin gwamnatin tarayya ko hukumominta da zai sabawa tanade-tanaden doka.