Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Harajin Cinikayya (VAT) Na Nan A Kan Kaso 7.5 Cikin 100 – Ministan Kudi


Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun
Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun

Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun ya musanta rade-radin da ake yi na cewar an kara harajin cinikayya(vat) daga kaso 7.5 zuwa kaso 10 cikin 100.

A yau Litinin, Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun ya musanta rade-radin da ake yi na cewar an kara harajin cinikayya(vat) daga kaso 7.5 zuwa kaso 10 cikin 100.

A sanarwar daya fitar, Ministan ya bada tabbacin cewar harajin cinikayyar (vat) da ake caza akan kayayyaki da ayyuka na akan kaso 7.5 cikin 100 kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin Najeriya akan haraji.

A cewar Wale Edun, “har hanyu harajin cinikayya (VAT) na nan akan kaso 7.5 cikin 100 kuma shine abinda gwamnati ke caza akan cinikayyar wani rukunin kayayyaki da ayyuka da harajin ke aiki akansu. Don haka, babu ko guda daga cikin gwamnatin tarayya ko hukumominta da zai sabawa tanade-tanaden doka.

“A zahirin gaskiya ma, sanin kowa ne cewar a baya-bayan nan gwamnatin tarayya, ta bada umarnin dakatar da karbar haraji akan nau’ukan kayan abinci irinsu shinkafa da alkama da wake da sauransu, a yunkurinta na samar da rangwame ga ‘yan najeriya da harkokin kasuwanci.

“Zan sake jaddadawa, har izuwa yau, harajin da ake caza akan cinikayya (VAT) na nan akan kaso 7.5 cikin 100 kuma shine abinda za’a cigaba da caji akan duk wata cinikayyar kaya ko aiki dake karkashin wannan haraji.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG