Majalisar Wakilan Jihar Plato Ta Kafa Kwamitin Binciken Matsalolin Tsaro

Yara marayu da suka rasa iyayensu

Bayan rigingimun da suka haddasa asarar rayuka masu yawa da dimbin dukiya majalisar wakilan jihar Plato ta kafa wani kwamitin bincike da zai gano musabbabin rikicin tare da zakulo hanyoyin magancesu

Majalisar Wakilan jihar Plato ta kafa wani kwamiti mai mutane bakwai da zai duba matsalolin tsaro a jihar da zummar magancesu.

Mai wakiltar Kantana a majalisar, Yusuf Gaddi shi ne shugaban kwamitin. Ya ce an karkashe mutane a kauyukansu da tituna ana ta yin zanga zanga akan lamarin. Yace su a majalisar wakilai sun kafa kwamitin ne, domin yi bincike su san dalilan da suka jawo abun da ya faru da kuma nazarin matakan da za’a dauka, domin irin wannan aika aikar bata sake faruwa ba.

Yace akwai mutanen da suka gudu suka shiga jeji, kuma har yanzu basu dawo ba. An kone gidajensu. Basu da abinci da kayan sawa. Akwai wasu kuma a asibitoci basu san inda ‘yan uwansu suke ba. Dole ne a yi bincike a san idan mutanen suke.

Haka kuma zasu bincika su san wadanda suka haddasa aika akar. Ba kaman da ba, zasu bukaci jami’an tsaro su bayyana wadanda suke da hannu a lamarin su kuma gayawa duniya hukumcin da aka yi masu.

Shugabar kungiyar matan Berom Ngo Chollom ta ce wasu daga cikin abubuwan da suke hadasa irin wannan iriciki, shine ana kutuntawa al’ummarsu. Sau tari makiyaya zasu hanasu noma ko kuma su lalata masu gonakinsu tare da yiwa mata fyade. Saboda haka basa iya zama kauyukansu. Baicin hakan akan shiga gidajensu ana harbe yara.

Shi ko Ardo Yabubu Dabo Boro sakataren harkokin kudi na kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Plato ya ce sace shanu da kashe al’ummar Fulani ke kawo tashin hankali a Plato. Ya ce sun sanar hukuma kuma an tabbatar cewa ana sace shanunsu. Yayinda aka yi kokari a fitar da shanun al’ummar Berom sun hana.

Shi kuma daraktan hukumar inganta zaman lafiya da sulhu a jihar Joseph Lenman, yace aiwatar da tsarin matakan da shugaban kasa ya kaddamar a jihar Plato zai taimaka sosai.

A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Jihar Plato Ta Nada Kwamiti Binciken Matsalolin Tsaro – 3’ 58”