"Kudurin da majalisar dokokin Jamus, ta amince da shi, zai yi illa ga dangantaka tsakanin Jamus da Turkiya," inji shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdgan, jim kadan bayan da majalisar ta kada wannan kuri'a.
Yayi magana ne a lokacin wani taron da manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya, Erdogan,yace bayan da kasar ta bukaci jakadar kasar a Jamus ya koma gida domin tattaunawa, kasar daga bisani zata duba matakai da zata dauka gaba, a zaman martani kan wannan kuduri.
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta gayyaci karamin jakadan Jamus zuwa helkwatarta bayan da majalisar dokokin Jamus ta amince da wannan kuduri.
Shugabar Jamus Angela Merkel, tace kasashen biyu suna kyakkyawar dangantaka mai zurfi, duk da banbance-banbance dake akwai kan wani batu guda daya tilo."