Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutane Miliyan 45 Ne Ke Cikin Bauta A Fadin Duniya


Wasu 'yan Burma da suke aikin kamun kifin dole a matsayin yin bauta
Wasu 'yan Burma da suke aikin kamun kifin dole a matsayin yin bauta

Wata kungiya daga kasar Australia, wacce take sa ido kan bauta irin ta zamanin yau, tace za'a iske kasashen da basa yaki da wannan al'ada, data shafi mutane kimanin milyan 45 a fadin duniya.

Galibi suna da irin gwamnatoci da suke goyon baya, ko suke kauda kai, ko suke fama da fitintinu ko rashin daidaito a cikin kasashen.

A cikin kasashen da kungiyar wadanda basa katabus wajen yaki da bautar, sun hada harda Koriya Ta Arewa, da Iran da Eritrea, da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da jamhuriyarDemokuradiyyar Kwango, da kuma Sudan ta Kudu. Yanayin bautar sun hada da tilastawa mutane yin aiki, a wasu gidajen fursina, da tilastawa mata shiga karuwanci domin riba, da tilastawa mata auren dole.

Kungiyar tace Koriya Ta Arewa ita take da adadin jama'arta da suke cikin wannan hali. Rahoton kungiyar yace India ce take da jama'a mafiya yawa, miliyan 18 da suke cikin bauta, China ta biyu nada mutane miliyan 3.39, sai kuma Pakistan wacce take da mutane miliyan biyu da digo 13.

Wannan adadi ya karu da mutane miliyan 10 tun a shekara ta 2014 lokacinda kungiyar ta gudanar da safiyonta na farko.

XS
SM
MD
LG