Majalisar Dokokin Ghana Ta Amince Da Dokar Noma Ganyen Wiwi Don Habaka Masana’antu Da Kiwon Lafiya

Majalisar Dokokin Ghana

Majalisar dokokin Ghana ta zartar da doka mai cike da ce-ce-ku-ce a wani matakin da zai taimakawa kasar shiga jerin kasashen da suke amfana da samun biliyoyin daloli daga masana’antar a duniya, ta wajen amincewa da dokar noma ganyen wiwi.

ACCRA, GHANA - Kudirin wanda aka yi wa kwaskwarima, bayan kotun kolin kasar ta dakatar da fara aiwatar da dokar da farko, inda tace sashe na 43 na dokar ya ci karo da sashe na 106 na kundin tsarin mulkin kasar, a halin yanzu ya baiwa ma’aikatar harkokin cikin gida ikon ba da lasisin noman tabar wiwi ga wadanda suka dace bayan shugaban kasa ya rattaba hannu a kai.

Ganyen Tabar Wiwi

Kakakin Majalisar dokoki, Rt. Hon. Alban Bagbin ya ce, bayan karatun dokar miyagun kwayoyin ta 2023, karo na uku, dukan 'yan Majalisar sun amince da dokar babu ko daya da yace a’a.

Nana Kweku Agyeman, shugaban kungiyar Hempire na Ghana, kungiyar dake fafutukar tabbatar da wannan doka, ya yi bayanin banbancin tabar wiwi da aka zartar da dokar nomawa a Ghana da kuma irin tabar wiwi da ake sha domin nishadi ko maye. Ya ce “tabar wiwi na masana'antu na girma zuwa tsayin kusan kafa 15, kuma ganyen siriri ne jikin reshe mai kauri kuma yana kunshe da sinadarin THC na 0.3 cikin 100; amma tabar wiwi na nishaɗi ko maye na tsayin kimanin kafa 7, kuma ganyen na da faɗi da wasu kwayoyi.”

Wata Gonar Tabar Wiwi A Ghana

Har yanzu dokar hani da shan tabar wiwi don maye da nishadi na nan, kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukuma, kamar yadda, Dr. Salisu Ango, likitan kwakwalwa da ilmin halayyar dan Adam ya yi kira ga matasa da kada su yi wa wannan doka rashin fahimta.

Wasu al’ummar Ghana sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da zartar da wannan kudurin da Majalisar dokokin ta yi.

Bayani akan irin ganyen tabar wiwi

Kasashen da suka zartar da dokar halatta noman tabar wiwi domin kiwon lafiya, kimiya da masana’antu sun hada da Zimbabwe, Afirka ta Kudu, Uganda, Malawi, Zambia, Rwanda, Uruguay, Kanada, da Thailand.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Ghana Ta Amince Da Dokar Noma Tabar Wiwi Don Habaka Masana’antu Da Kiwon Lafiya.mp3