Yarjejeniyar da ake kira “Ba dai-daito” wacce Firaminista Thersa May taki amincewa da ita, a bangare daya kuwa ‘yan majalisar kasar sun ki amincewa da yarjejeniyar da May ta cimma da sauran kasashen kungiyar ta Turai.
A jiya Talata ‘yan majalisun sun kada kuri’ar amincewa da a sake duba yarjejeniyar. "Adadin wadanda suka kada kuri’ar amincewa a hannun dama, dari biyu da arba’in da biyu (242). Wadanda suka kara kuri’ar kin amincewa a haggu dari uku da casa’in da daya (391). Saboda haka wadanda suka ki amincewa sun yi rinjaye."
Idan kuma har ‘yan majalisun suka ki amincewa daficewa Ba-dai-daito, to za’a kada kuri’a ta uku a ranar Alhamis, wanda za’a bukaci kungiyar ta kara lokaci daga ranar 29 don sake duba wasu hanyoyi da za’a bi a fice.
Tilas ne kasashen kungiyar Tarayyar Turai su amince da duk wani Karin wa’adi da za a bukata.