Majalisar Dokokin Armenia Ta Zabi Nikol Pashinian A Matsayin Firai Ministan Kasar

Wannan zaben na zuwa ne bayan makonnin da aka kwashe ana zanga-zanga a kasar.

Karshenta dai, majalisar dokokin kasar Armenia ta zabi madugun ‘yan adawa Nikol Pashinian ya zama sabon Firaministan kasar.

A zaman da aka yi a yau Talata ne, sabon Firaministan ya lashe zaben da aka gudanar a majalisar da goyon bayan ‘yan majalisa 59, yayinda abokan takararsa suka karkare da goyon bayan ‘yan majalisa 42.

Shi dai Pashinian shine yayi jagorancin gangamin jama’a na zanga-zangar lumana da aka yi wa tsohon Firaminista Serz Sargsyan, bayan da aka zarge shi da kokarin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima don kada ya sauka daga kan karagar mulki.