A hukumance, Majalisar Dokokin Amurka ta ki amincewa da dokar ta-baci da shugaba Donald Trump ya ayyana don samun kudin da zai gina katanaga, yayin da ‘yan majalisar dattawa suka jefa kuri’a 59 - 41 ta kin amincewa da karfin ikon shugaban kasa da ya yi amfani da shi.
A 'yan makwannin da suka gabata ne ita ma majalisar wakilai ta dauki irin wannan mataki.
Sanatoci 12 na jam’iyyar Rifoblikan sun hada kai da ‘yan jam’iyyar Dimokrata inda suka fatali da matakin a majalisar mai rinjayen ‘yan Republican.
Wannan mataki, ya yi watsi da bukatar White House tare da yin biris da barazanar da shugaba Trump ke yi na amfani da karfin ikonsa wajen yin gashin-kansa kan wannan lamari.
“Wannan zabe na musamman – ba haka aka saba ba,” a cewar shugaban marasa rinjaye Chuck Schumer, dan jam’iyyar Dimokrat daga New York, yana mai nuni da yadda a hukumance majalisa a karon farko ta yi watsi da ayyana dokar ta bacin.
A can Fadar White House kuwa, Trump ya yi alkawarin zai bayyana matsayarsa kan wannan kudirin dokar.