Majalisar Dinkin Duniya Ta Zargi Dakarun Myanmar Da Kokarin Korar Musulmin Rohingya Daga Yankin Har Abada

A newly arrived Rohingya girl carries food rations in Kutupalong, Bangladesh, Saturday, Sept. 30, 2017.

Nan take Jami'an Myanmar basu maida murtani akan rahoton na Majalissar Dinkin Duniya ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashin hankalin dake faruwa a Jihar Rakhine na yammacin kasar Myanmar, bangare ne na wani kyamfe da sojojin gwamnatin kasar suka kaddamar da nufin korar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya daga yankin har abada.

Wani rahoton da ofishin kare hakkin bil Adama na MDD ya bayar yau laraba a birnin Geneva, ya zargi sojojin Myanmar da ‘yan daba mabiya addinin Buddha, da laifin Konawa da rushe gidaje da kauyukan ‘yan Rohingya, har ma da kokarin kawar da duk wata alamar kasancewar Musulmi ‘yan Rohingya a wannan wuri.

‘Yan gudun hijira fiye da rabin miliyan sun tsallaka zuwa Bangladesh tun daga 25 ga watan Agusta a bayan da jami’an tsaron Myanmar suka fara kai munanan hare-haren da suka ce maida martani ne ga wani harin da ‘yan Rohingya suka kai musu. Amma rahoton na MDD yace an fara daukar matakan kawar da ‘yan Rohingya wata guda kafin wannan harin da aka yi zargi.