Babban Kwamishinan hukumar kare hakkin dan adam a Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra’ad Al Hussein, ya nemi da a ba shi damar zuwa kasar Kamaru, domin ya gudanar da bincike kan zargin mummunan cin zarafin bil Adama da ‘yan aware da dakarun gwamnati ke aikatawa a yankunan kudu maso yammaci da arewa maso yammaci da ke amfani da harshen Ingilishi.
Mai magana da yawun babban kwamishinan, Ravina Shamdasani, ta fadawa Muryar Amurka cewa rikicin yankin wanda ya faro daga zanga zangar neman adalci wajen samun ayyukan yi da harshen da ake amfani da shi, ya rikide ya koma wani babban al’amari.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, sun nuna cewa sama da ‘yan gudun hijira dubu 21 sun tsere zuwa kasashe makwabta, yayin da mutum dubu 160 suka rasa muhallansu sanadiyar rikicin, inda rahotanni suka nuna cewa akwai da yawa daga cikinsu da ke boye a cikin dazuka.
Sai dai wani kakakin rundunar sojin kasar ta Kamaru, ya musanta wadannan zarge-zarge da aka ce dakarun kasar sun aikata, yana mai cewa duk zuki-ta-malle-ne.