Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Adawar Zimbabwe MDCA Ta Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Zabe Mai Zuwa


Babbar Jam'iyyar adawa ta Zimbabwe ta yanke shawarar cewa ba zata kauracewa zaben da za'a gudanar mako mai zuwa ba, amma har yanzu tana ganin hukumar zaben ta shirya yin magudi da sakamakon ga jam'iyya mai mulki.

Shugaban jam'iyyar adawa ta Movement for Democratic Change Alliance MDCA’ Nelson Chamisa, ya gayawa manema labarai a wani taron manema labarai jiya Laraba cewa yana da tabbacen lashe zaben shugabancin kasar Zimbabwe a zaben ranar Litinin mai zuwa.

Ba zai yiwu mu kauracewa nasarar mu ba, abin da waddanda basa son mu ci zabe ke so mu yi kenan. Al'umma na son mu ba masu mulkin kama karya kashi, mu shawo kan talauci, mu shawo kan cin zarafi, mu samarwa al'umma kyakyawan makoma. Nasarar mu tabbas ne! - ya kamata ku san haka.


Hukumar zaben tayi watsi da bukatar jam'iyyar adawa na ganin an yi amfani da kuri'u a zaben, jam'iyar adawa ta ce jefa kuri'ar zai taimakawa shugaba Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF wajen ajiye shi a wani matsayin da zai bashi dama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG