A cikin wata doguwar sanarwa da membobin kwamitin duka goma sha biyar suka amince da ita, an bayyana matukar damuwa akan barkewar cutar kwalara kwanan nan, da kuma yiwuwar fuskantar yunwa.
Kwamitin sulhun ya jadada cewa, za a iya warware rikicin na kasar Yemen ne kawai ta wajen komawa gudanar da harkokin siyasa dake damawa da kowa, tare kuma da kira ga bangarorin dake rikici da juna su dauki matakan wanzar da zaman lafiya, bisa ga sanarwar da shugaban kwamitin sulhun Sacha Llorentty na kasar Bolivia ya karanta.
Yunkurun Majalisar Dinkin Duniya na wanzar da zaman lafiya ya gamu da cikas, inda makonni biyu da suka shige, manzon musamman na babban magatakardar Majalisa Dinkin Duniya ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki a rikicin har yanzu basu shirya daukar matakan da suka kamata na cimma matsaya ba.