Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Gargadin Ficewa Daga Hukumar Kula Da 'Yancin Bil Adama


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta yi gargadin cewa Amurka zata fice daga cikin hukumar kula da 'yancin Bil Adama ta Majalisar idan har hukumar bata yi wasu sauye-sauye ba.

Nikki Haley, wadda kuma ta ke cikin ministocin shugaba Donald Trump, tana bayyana ra’ayinta akan abin da tace mambobin hukumar na nuna son zuciya akan akan Isra’ila.

Jakadiya Haley, ta ce “Tun lokacin da aka kirkiri hukumar, ta zartar da kudurori sama 70 akan Isra’ila. Kuma ta zartar da kudurori bakwai kawai kan kasar Iran.”

Haka kuma Haley, ta soki ita kanta Majalisar Dinkin Duniya kan abin da ta kira son zuciya kan Isra’ila.

Amurka da Isra’ala sun sha sukar lamirin MDD kan mayar da hankali kan kasar yahudawa kadai, wanda suka ce kamata yayi ta mayar da hankali kan kasashen da ke take hakkin bil Adama ko taimakawa ayyukan ta’addanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG