Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Larabawa Shida Sun Yanke Huldar Diflomasiya da Kasar Qatar


 SarkinQatar Emir Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani
SarkinQatar Emir Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani

Bisa zargin cewa kasar Qatar mai arzikin man fetur na goyon bayan akidar ta'addanci ya sa wasu kasashen larabawa shida suka yanke huldar diflomasiya da ita tare da dakatar da zirga zirgan jiragen sama tsakaninta da kasashen larabawan

Yau kasashe shidda da suka hada da Saudi Arabia, Misra, Bahrain, Junhuriyar Demokradiyyar Larabawa, Yemen da Maldives duk sun tsinke dangatakar diplomasiya da kasar Qatar, bayan da suka zarge ta da cewa tana bada goyon baya ga akidar ta’addanci.

Sai dai ma’aikatar harakokin wajen Qatar ta bayyana wannan matakin da cewa “baya da hujja kuma mataki ne da aka dauka a bisa zargi maras tushe.”

Kasashen shidda sunce zasu janye ma’aikatansu na jakadanci sannan kuma sun tsinke duk wata zirga-zirgar sufurin jiragen sama da kasar ta Qatar mai arzikin man fetur.

Shima kampanin jiragen saman na Qatar Airways ya bada sanarwar cewa ya tsaida jiragensa daga zuwa Saudi Arabia.

Misra ta yanka wa jakadan Qatar wa’adin awowi 48 da ya bar mata kasarta yayinda sauran kasashen na yankin Gulf suka yanka wa ‘yan kasar Qatar dake zaune a kasashensu wa’adin kwannaki 14 na su tattara nasu-ya-nasu, su bar musu kasashensu.

Haka kuma Saudi Arabia, wacce ke jagorancin kasashen dake goyon bayan gwamnatin Yemen da sojojinsu a yakin da ake can Yemen din, ta nemi Qatar ta fitar da sojanta daga kawancen na soja.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG