Majalisar Dinkin Duniya Ta Horas Da Matasa 100 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Majalisar dinkin duniya ta horas da matasa dari daga jihohin arewa maso gabashin Najeriya, kan matakan da zasu bi wajan cudanya da al’umma, da rungumar kasuwanci domin dogaro da kai da kawar da zaman kashe wando.

Hoaron na makonni biyu da cibiyar kayar da dabarun zama dan kasa na gari ta bayar a Jos, jihar Plateau, ta tattaro matasa ne daga jihohin Adamawa, da Borno da jihar Yobe da kuma jihar Gombe, wadanda suka sha fama da rikicin Boko Haram, dana ‘yan kalare.

Matasan dai dai da dai dai sun bayyana ra’ayoyinsu a matsayin wadanda suke alfahari da horaswar da suka samu da bayyana farin cikinsu musamman akan yadda aka koya masu hanyoyin dogaro da kai da kuma cudanya da juna, da kuma sana’o’in da basa yiyuwa sai da hadin giwar abokan sana’a da hakuri da juna sauransu.

Wakilin majalisar dinkin duniya me kula da shirin bada tallafi dan inganta rayuwar al’umma Kehinde Bolaji, ya ce manufar shirin itace domin a tallafawa al’ummomin da suka fada cikin bala’i domin dawowa cikin haiyacinsu, su kuma sake samun rayuwa me inganci.

A jawabinsa ya ce “mun taimaka da shirin bada kudade domin karfafawa matasa masu sana’ar hannu gwiwa, ta yadda zasu koma domin bada gudummuwa wajan sake gina yankunansu.”

Shugaban kungiyar koyar da dabarun zama dan kasa na gari dake Jos, Abdulmumini Adamu Maimako, ya bayyana cewa sun koyawa matasan dabi’u masu kyau da zasu taiamaka masu a rayuwa.

Domin Karin bayani saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dinkin Duniya Ta Horas Da Matasa 100 A Arewa Maso Gabashin Najeriya